Sunday, 24 July 2016

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJU'UN 

Wannan labari ya faru ne a cikin garin Damaturu 

Wata mata mai kimanin shekaru 40 da yaro 'Dan shekara 9 taje gurin masusayar da masara tace abata masara kwano biyi wato mudu biyu sai akace mata 600 sai tace eh ta sani a gwada mata bayan an auna sai ta karba tace bari ta miqawa masu niqa zata bar yaronta idan ta dawo daga gurin niqan zata biya ta dauki yaronta sai mai sayar da masarar yace ai babu matsala sai ta dawo
.
aka baiwa yaro gurin zama ya zauna aka shafe lokaci mai tsawo wannan mata bata dawo ba sai yaro ya fara kukan yunwa aka bashi abinci yaci har lokacin uwar bata dawo ba sai mutanen gurin suka tambayi yaron cewa wannan matar mamanka ce ? Sai yaro yace eh mamansa ce sai mutanen suka qara tambayar sa cewa kasan gidan Ku ? Sai yaro yace eh sai sukace to muje mutane uku ciki harda mai sayar da masarar suka sa yaro agaba zuwa gidan su yaro a Unguwar Nayi-Nawa acikin grain Damaturu sukayi sallama suka shiga sai suka tawar da wani dattijo bayan sun gaisa sai suka tambayi dattijon cewa ko yasan wannan yaro ? sai dattijo yace 'Dana ne kuma dama nasan zakuzo nine na tura uwarsa cewa taje ta auno mana masara ta barshi agurin mai masarar domin ko yayi zaton zata dawo sai tsohonnan ya fashe da kuka yace yau kimanim kwana hudu kenan ba'a dora tukunya a gidannan ba kullum sai dai na fita bayan gari na ciro tafasa ko wani ganye a dafa muci inada yara 5 yanzu wannan masara dana tura uwar wannan yaro ta auno haka aka dafa mana ita mukaci saboda bamu da halin sarrafata zuwa gari sai tausayi yasa wayannan mutane suka kama kuka har sukayi musu Alheri
.
Nayi matuqar kaduwa da samun wannan labari Lallai Sai mun koma ga Allah sannan Allah zai yaye mana wannan hali da muke ciki

No comments:

Post a Comment