Friday, 10 June 2016

Zanga Zangar Dalibai A Kwalejin FCE Ta Gombe

Wasu Yan Sanda Na Kula Da Masu Zanga Zanga
A jihar Gombe hukumar gudanarwar kwalejin ilmi ta gwamnatin tarayya, ta rufe kwalejin har sai abin da hali yayi.
Wannan hukunci da hukumar kwalejin ta dauka ya biyo bayan tarzoma da kuma tada kayar baya da daliban kwalejin suka gudanar a yau, sanadiyar rashin ruwa da wutar lantarki.
Rahotanni na bayanin cewa ‘daliban sun lalata gine gine da kuma motocin kwalejin, wanda hakan ya tilastawa jami’an tsaro yin amfani da bindiga da kuma barkonan tsohuwa.
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Gombe dai ta samu labarin ‘daliban kwalejin tarayya, suna zanga zanga akan rashin ruwa wanda hakan yasa jami’an yan sanda sukayi gaggawa domin zuwa makarantar inda suka tarwatsasu, sai kafin isarsu ‘daliban sunyi barna sosai, inji DSP Ahmed Usman kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Gombe.

No comments:

Post a Comment